Sojojin Gwamnatin Somaliya Sun Kashe Wani Babban Kwamandan Kungiyar Al-Shabab
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9583-sojojin_gwamnatin_somaliya_sun_kashe_wani_babban_kwamandan_kungiyar_al_shabab
Mahukuntan Somaliya sun tabbatar da labarin kashe daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab a yankin Hiran da ke yammacin garin Beledweyne a kudu maso tsakiyar kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:45+00:00 )
Aug 13, 2016 12:56 UTC
  • Sojojin Gwamnatin Somaliya Sun Kashe Wani Babban Kwamandan Kungiyar Al-Shabab

Mahukuntan Somaliya sun tabbatar da labarin kashe daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab a yankin Hiran da ke yammacin garin Beledweyne a kudu maso tsakiyar kasar.

Mataimakin gwamnan garin Hiran Muhammad Ibrahim Abdullahi a yau Asabar ya bayyana cewa: Dakarun sa-kai da suke tallafawa sojojin gwamnatin Somaliya sun yi bata kashi da mayakan kungiyar Al-Shabab a yankin Luuq Jeelow da ke nisan kilomita 20 da garin Beledweyne, inda suka yi nasarar kashe mayakan kungiyar Al-Shabab hudu ciki har da Abdi Adni daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Al-Shabab.

Kwamandan rundunar sojin Somaliya ta musamman ta Somalia National Army {SNA} a takaice Janar Umar Adan Hassan ya sanar da cewa: Rundunar sojin Somaliya zata ci gaba da tallafawa dakarun sa- kai a kokarin da suke yi na kare kansu daga hare-haren wuce gona da irin kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab.   .