Kame Wani Kusa Na 'Yan tawayen Kasar Rwanda A D-Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9619-kame_wani_kusa_na_'yan_tawayen_kasar_rwanda_a_d_congo
An kame daya daga cikin jagororin 'yan tawayen kasar Rwanda a gabacin kasar D-Congo
(last modified 2018-08-22T06:58:45+00:00 )
Aug 14, 2016 10:28 UTC
  • Kame Wani Kusa Na 'Yan tawayen Kasar  Rwanda A D-Congo

An kame daya daga cikin jagororin 'yan tawayen kasar Rwanda a gabacin kasar D-Congo

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar  Sin ya ce; An Kame Sabimana Iraguha wanda daya ne daga cikin jagororin kungiyar 'yan tawayen kasar Rwanda ta ( FDLR) a yankin Katiru da ke gundumar Kivo ta Arewa da ke gabacin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Dama dai tuni ana neman Iraguha ruwa a jallo saboda laifukan kishan Kiyashi a kasar Rwanda, da kuma kashe sojojin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Kwamandan bangaren sadarwa na sojojin D-Congo mai suna Guillaume Kaiko ya ce; Iraguha ya kashe sojojin kasar 32 a ranar 14 ga watan Mayu na 2013 a kauyen Bunyakiri da ke gundumar Kivo ta Kudu.

Sojojin kasar ta D-Congo sun yi kira ga dukkanin 'yan tawayen da ke gabacin kasar da su mika kai.

Gabacin kasar D-congo dai tunga ce ta 'yan tawayen cikin gida da kuma na kasashen makwabta.