Wani Sabon Rikici Ya Barke A Kasar Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9622-wani_sabon_rikici_ya_barke_a_kasar_sudan_ta_kudu
Rahotanni daga kasar Sudan ta kudu suna nuni da cewa wani sabon rikicin da musayen wuta ya barke a yankin Yei dake kudu maso yammacin kasar tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye karkashin jagoranci tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.
(last modified 2018-08-22T06:58:45+00:00 )
Aug 14, 2016 12:51 UTC
  • Wani Sabon Rikici Ya Barke A Kasar Sudan Ta Kudu

Rahotanni daga kasar Sudan ta kudu suna nuni da cewa wani sabon rikicin da musayen wuta ya barke a yankin Yei dake kudu maso yammacin kasar tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye karkashin jagoranci tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.

Kamfanin  dillancin labaran Reuters ya  bayyana cewar mummunan rikici da kuma musayen wuya ya barke tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a yankin Yei da ke kusa da kan iyakan Sudan ta Kudu da kasar Uganda lamarin da ya kara dagula lamurra a kasar a kokarin da ake yi na kawo karshen rikicin na baya-bayan nan da yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa da kuma tilaswa wa wasu dubbai zama 'yan gudun hijira.

A wata sabuwa kuma gwamnatin kasar Sudan ta kudu ta sanar da cewa za ta sake dubi cikin matsayar da Majalisar  Dinkin Duniya ta dauka na tura sojoji zuwa Sudan ta Kudu don kawo karshen wannan rikicin sakamakon sake barkewar wannan rikici.

Ministan watsa labaran Sudan ta Kudun Michael Makuei ne ya sanar da hakan bayan zaman majalisar ministocin kasar inda  ya ce bayan dubi sosai cikin takardun MDD, gwamnatin ta gano lalle akwai matsaloli cikin takardun da wajibi ne a sake dubi cikinsu.

MDD dai ta kuduri aniyar tura wasu karin sojoji zuwa Sudan ta Kudun ne bayan barkewar wani sabon rikici  a birnin Juban, babban birnin Sudan ta  kudu a  kwanakin baya.