Aug 15, 2016 05:41 UTC
  • Fara Yakin Neman Zaben Shugabancin Kasar Gabon

Hukumar zaben kasar Gabon ta sanar da ranar Asabar 13 ga wannan wata na Agusta a matsayin ranar fara yakin neman zaben shugabancin kasa kwanaki 15 kafin ranar gudanar da zabe a duk fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa daga Libreville fadar mulkin kasar Gabon ya habarta cewa: Hukumar zaben Gabon ta ware kwanaki 15 a matsayin ranakun gudanar da yakin neman zaben shugabancin kasar, kuma tuni hukumomin tsaron Gabon suka yi gargadi kan kiyaye doka da oda a lokacin gudanar da yakin neman zaben shugabancin kasar da za a gudanar da ranar 27 ga wannan wata na Agusta da muke ciki.

Yan takara 14 ne zasu fafata a zaben shugabancin kasar ta Gabon bayan da hukumar zaben kasar ta soke takardar neman takarar mutane biyar sakamakon jinkirin biyan kudaden lamuni a asusun hukumar zaben kasar da yawansu yakai dalar Amurka 33,505.

Daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar Gabon a wannan karo har da Jean Ping shahararren dan siyasa a kasar ta Gabon kuma tsohon shugaban kungiyar tarayyar Afrika ta AU, sannan akwai tsoffin fira ministocin kasar guda biyu, sannan akwai tsohon shugaban Majalisar Dokokin Kasar ta Gabon da sauran manyan 'yan siyasa, sai dai wasu alkaluma suna ganin Jean Ping a matsayin dan adawa mafi karfi da zai kalubanci shugaban kasar mai ci Umar Bongo Ondimba a yayin zaben shugabancin kasar a wannan karo.

Tuni dai kotun kare kundin tsarin mulki kasa ta Gabon ta wanke shugaban kasar Umar Bongo daga zarge-zargen da 'yan adawa suke yi masa na rashin cancantar tsayawa takarar shugabancin kasar ciki har da zargin cewa: An haifi Umar Bongo ne a wajen kasar alhalin sakin layi na 10 na kundin tsarin mulkin kasar ya bayyana cewa dole ne shugaban kasa a Gabon ya kasance haifaffen cikin kasar Gabon.

Har ila yau 'yan adawa a kasar Gabon suna ci gaba da bayyana fargabarsu kan yiyuwar tafka magudin zabe lamarin da ya sanya ofisoshin jakadancin kasashen faransa da Amurka gami da wakilin kungiyar tarayyar Turai suka fitar da bayanin hadin gwiwa suna kira ga gwamnatin Gabon kan gudanar da zaben cikin 'yanci da adalci. 

A nashi bangaren shugaban kasar Gabon Umar Bongo Ondimba ya gargadi 'yan adawa da su guji kunna wutan rikici da tashe- tashen hankula a kasar, yana mai zargin wasu jam'iyyun adawa da kokarin tunzura jama'a domin janyo rudani da rashin kwanciyar hankali a bayan zabuka a kasar. 

Tags