An Kashe Mayakan Boko Haram 16 A Tarayyar Nigeria.
Aug 16, 2016 02:03 UTC
Sojojin Nigeria sun kashe mayakan boko haram 16 a jihar Borno.
Majiyar sojojin tarayyar Nigeria ta bayyana cewa sojojin kasar sun sami nasara kashe mayakan boko haram 16 a wasu sumamen da suka kai masu a jiyar Borno arewa maso gabcin kasar. Kamfanin dillancin labaran shinhuwa na kasar China ya nakalto Sani Usman kakakin sojojin kasar yana fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa a sumamen da sojojin suka kai sun tilastawa mayakan boko haram jada baya, sun kuma kashe 16 daga cikinsu , sannan dansanda guda da kuma sojoji 11 sun ji rauni.
Kakakin sojojin ya kammala da cewa sojojin kasar zasu ci da aikinsu na bin duggugin mayakan na boko haram har zuwa ganin bayansu.
Tags