Adadin Fararen Hula Da Aka Kashe A Kongo Kinshasa Ya Kai 51
Aug 16, 2016 06:43 UTC
Rahotanni daga Jamhuriya demukuradiyyar Kongo na cewa farar hula 51 ne suka rasa rayukansu bayan harin da wasu mayaka suka kai a birnin Beni dake gabashin kasar.
Mr Teddy Kataliko, wani mamba a kawancen kungoyoyin fara na yankin ya shaidawa kanfanin dilancin labarai na AFP cewa sun kirga gawawakin mutane 51 da aka kashe da adda.
Ana dai zargin 'yan tawayen Uganda da kai harin na daren Asabar zuwa Lahadin data gabata.
A wani labari dai babban sakatare na MDD Ban Ki-moon ya ce ya girgiza sosai kan wannan lamarin, tare da yin Allah wadai da harin da babbar murya. Haka kuma, ya jajanta wa iyalan wadanda suka mutu da kuma gwamnatin Kongo Kinshasa.
Tags