An Kame Mutane Fiye Da 100 A Kasar Zambia
Rikicin Bayan Zabe A Kasar Zambia
'Yan sandan kasar Zambia Sun kame mutane 150 da su ke nuna kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa.
Kamfanin Dillancin Labarun Farasna daga birnin Lusaka ya ambato wani jami'in 'yan sanda Godwn Phiri yana fada a yau talata cewa; Bayan sanar da shugaban kasar Edgar Lungu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi, an kame mutane 150 da su ka fito domin nuna kin amincewa da sakamakon zaben.
Jami'in 'yan sandan ya kara da cewa; Mutanen kudancin kasar ta Zambia sun yi imani da cewa jagoran 'yan hamayya, Hakainde Hichilema’ ne ya ci zaben, saboda haka su ka fito yin zanga-zangar kin amincewa da sakamakon da aka sanar.
Magoya bayan Hakainde Hichilema a kudancin Kasar sun fito kan tituna a jiya litinin da aka sanar da sakamakon zaben, inda su ka rika kona tayoyi da rufe hanyoyi.
Dan takarar shugaban kasar Hakainde Hichilema a karkashin jam'iyyar United Party of National Development party (UPND) ya yi watsi da sakamakon zaben da aka yi a ranar alhamis wanda kuma a jiya litinin aka sanar da sakamakon karshe.