Kame Wasu Gungun 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish A Kasar Maroko
Mahukuntan kasar Marako sun sanar da kame wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish da suke shirye-shiryen kaddamar da hare-haren ta'addanci a garin Daru -Bayda cibiyar kasuwancin kasar Maroko.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Maroko a jiya Talata ta fitar da sanarwar cewa: Jami'an tsaron kasar sun samu nasarar kame wasu gungun mutane hudu mambobi a kungiyar ta'addanci ta Da'ish da suke shirye-shiryen aiwatar da hare-haren ta'addanci a yankin da ke tsakanin garin Daru- Bayda da Mukrin.
Sanarwar ta kara da cewa: A binciken da aka gudanar kan gungun 'yan ta'addan an samu tabbacin cewa hare-haren da suke shirin kaddamarwa kan garin Daru -Bayda suna da hatsarin gaske lamarin da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa.