WHO Ta Kaddamar Da Rigakafin Cutar Zazzabin Shawara A Kasashen Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9763-who_ta_kaddamar_da_rigakafin_cutar_zazzabin_shawara_a_kasashen_afirka
Hukumar lafiya ta duniya WHO, tare da hadin gwiwar hukumomin agaji na kasa da kasa sun fara gudanar da allurar riga kafin cutar zazzabin shawara mafi girma a kasashen Angola da jamhuriyar demokaradiyyar Kongo a wannan mako.
(last modified 2018-08-22T06:58:46+00:00 )
Aug 17, 2016 06:34 UTC
  • WHO Ta Kaddamar Da Rigakafin Cutar Zazzabin Shawara A Kasashen Afirka

Hukumar lafiya ta duniya WHO, tare da hadin gwiwar hukumomin agaji na kasa da kasa sun fara gudanar da allurar riga kafin cutar zazzabin shawara mafi girma a kasashen Angola da jamhuriyar demokaradiyyar Kongo a wannan mako.

Mai Magana da yawun MDD yace an fara gudanar da rigakafin cutar ne domin dakile yaduwar annobar data barke, wace kuma ta hallaka sama da mutane 400.   

Mataimakin mai Magana da yawun MDD Frahan Haq, ya fada a taron manema labaru cewar, cutar zazzabin shawaara ta bazu ne a manyan garuruwa dake da cunkoson jama'a, da wasu birane, kana tana kokarin tsallakawa zuwa makwabtan kasashe, don haka ya zama dole a gudanar da riga kafin dakile yaduwar cutar.

Ya ce tuni aka samar da alluran riga kafin zazzabin shawarar ga mutane sama da miliyan 13 a kasar Angola, da kuma mutane miliyan 3 a demokaradiyyar Kongo, duk da a cewar kuma har yanzu akwai yankuna da ake fargabar yiwuwar fuskantar cutar.