RDC : Jami'an Tsaro Sun Murkushe Masu Zanga-zanga
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9766-rdc_jami'an_tsaro_sun_murkushe_masu_zanga_zanga
'Yan sanda da sojoji a Jamhuriya demukuradiyyar Kongo, sunyi amfani da hayaki mai sa kwalla da kuma harbin tsoratarwa domin tarwatsa masu masu zanga zanga a Beni.
(last modified 2018-08-22T06:58:46+00:00 )
Aug 17, 2016 06:34 UTC
  • RDC : Jami'an Tsaro Sun Murkushe Masu Zanga-zanga

'Yan sanda da sojoji a Jamhuriya demukuradiyyar Kongo, sunyi amfani da hayaki mai sa kwalla da kuma harbin tsoratarwa domin tarwatsa masu masu zanga zanga a Beni.

Mutanen yankin dai na zanga-zanga ne domin kalubalantar gwamnatin kasar akan rashin tabaka komai akan rikice rikice dake shafar yankin.

Wannan dai na zuwa ne a kwana na karshe na zamen makoki da ake a kasar bayan kisan da wasu mayaka da ake zargi da cewa 'yan Uganda ne suka kai a wannan yankin na Beni dake gabashin kasar inda suka kashe mutane 51.