Najeriya : 'Yan Sanda Sun Hana Taron PDP A Fatakwal
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9769-najeriya_'yan_sanda_sun_hana_taron_pdp_a_fatakwal
'Yan Sanda a birnin Fatakwal na Najeriya sun killace fillin kwalon Sharks da Jam’iyyar PDP ke shirin gudanar da taron ta na kasa yau laraba.
(last modified 2018-08-22T06:58:46+00:00 )
Aug 17, 2016 06:51 UTC
  • Najeriya : 'Yan Sanda Sun Hana Taron PDP A Fatakwal

'Yan Sanda a birnin Fatakwal na Najeriya sun killace fillin kwalon Sharks da Jam’iyyar PDP ke shirin gudanar da taron ta na kasa yau laraba.

Kamfanin dilancin labaran Najeriya ya rawaito cewa jami’an tsaro sun hana mahalarta taron da 'yan jaridu shiga fillin da aka shirya taron.

Manema labarai a yankin sun rawaito kakkakin ‘yan sanda jihar ta Rivers, Nnamdi Omoni na tabbatar da haka tare da cewa sunyi hakan ne bisa umarni kotu.

A jiya ne dai babbar kotun Abuja ta haramta gudanar da taron, wanda kuma ke zuwa bayan da wata babbar kotun Fatakwal ta bayar da umarnin a yi taron.

kafin hakan dai an yi tsammanin daidaita bangarorin da ba sa ga maciji da juna a Jam'iyyar wato Sanata Ali Modu Sheriff da Sanata Ahmed Makarfi a taron.