Shugaban Zambia ya dauki kudirin bunkasa kasar.
Shugaban Kasar zambia ya dauki kudirin bunkasa kasar a cikin shekaru biyar masu zuwa
A yayin da yake gudanar da jawabi gaban duban magoya bayan sa a filin wasa na The Woodlands dake Lusaka babban birnin kasar, Shugaban kasar Zambiya kuma Shugaban Jam'iyar PF Edgar Lungu ya ce yanzu babu wani abu da zai sanya a gaba face bunkasa da ci gaban kasar tare kuma da hada kan Al'umma.
A wani bangare na jawabinsa Shugaba Edgar Lungu ya bukaci jam'iyun Adawa da su kontarwa magoya bayan su hankali domin kaucewa rikici da tashin hankali a cikin kasar, kuma Shugaban ya ce za a jinkirta rantsar da shi wa’adi na biyu sakamakon karar da abokin takarar sa Hakainde Hichilema ya shigar a kotu saboda zargin magudi.
Bayan sanar da sakamakon zaben na Zambiya, magoya bayan 'yan adawa sun bazu a kan tituna da kuma kai hari a kan gine-ginan Gwamnati, inda suke zarki Gwamnati da tabka magudi a zaben Shugaban kasar.
Bisa rahoton 'yan sandar kasar sama da mutane 130 ne aka kame a yayin zanga-zangar, Dan takarar Jam'iyyar UPND da ya kalubalanci Shugaban Edgar Lungu ya zargi jam'iyar PF da yin aringizon kuri'u a wasu mazabu na Lusaka babban birnin kasar da kuma wasu manyan buranan kasar, inda ya bukaci da a sake gudanar da zabe.
A ranar 11 ga wannan Wata na Agusta da muke cikin ne Al'ummar kasar Zambiya suka gudanar da zaben Shugaban kasa gami da na 'yan Majalisun dokoki.