Sabon Mataimakin Shugaban Sudan ta kudu ya galgadi Madugun 'yan tawayen kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9781-sabon_mataimakin_shugaban_sudan_ta_kudu_ya_galgadi_madugun_'yan_tawayen_kasar
Sabon Mataimakin Shugaban Sudan ta kudu ya galgadi Madugun 'yan tawayen kasar da ya bar kasar ta zauna lafiya
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 17, 2016 13:37 UTC
  • Sabon Mataimakin Shugaban Sudan ta kudu ya galgadi Madugun 'yan tawayen kasar

Sabon Mataimakin Shugaban Sudan ta kudu ya galgadi Madugun 'yan tawayen kasar da ya bar kasar ta zauna lafiya

A wani jawabi da ya gabatar a wannan Laraba, sabon Mataimakin Shugaban kasar Sudan ta kudu Taban Deng Gai ya ce wajibi ne tsohon mataimakin shugaban kasar kuma madugun 'yan tawaye Riek Machar da ya fitar da hanunsa daga harakokin siyasar kasar domin a samu sulhu da konciyar hankali a tsakanin Al'umma.

Har ila yau Taban Deng Gai ya bukaci Riek Machar dake a matsayin mai gidansa a baya da ya dauki darasi a kan kura kuran da ya yi a baya.

har ila yau sabon Mataimakin shugaban kasar sudan ta kudun ya kara da cewa idan Riek Machar yana ganin ba zai iya gudanar da rayuwarsa cikin konciyar hankali a kasar ba to yana iya zuwa kasar Kenya ko kuma wata kasa daga cikin kasashen  Afirka ya jira zaben 2018.

A shekarar 2013 ne shugaba Salva Keir na  Sudan ta kudu ya zarki mataimakin sa  Riek Machar da yunkurin juyin milki, lamarin da ya janyo yakin basasa a kasar inda duban fararen hula da sojoji suka rasa rayukansu, bayan shiga tsakani na kasashen Duniya an samu fahimatar juna tsakanin bangarorin biyu a karshen shekarar da ta gabata, inda Riek Machar ya sake komawa birnin Juba kuma ya karbi mukaminsa na Mataimakin shugaban kasa, sai dai kuma a watan jiya wani rikicin ya sake barkewa bayan da bangaren shugaba Salva Keir ya yi yunkurin   kawar da Riek Machar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 300 yayin da wasu dubai suka yi gudun hijra zuwa kasashen dake makobtaka da kasar.