MDD Ta Damu Kan Rashin Kudin Ayyukan Jin Kai A Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9802-mdd_ta_damu_kan_rashin_kudin_ayyukan_jin_kai_a_sudan
Majalisar dinkin duniya, ta sanar da damuwar ta akan makekin gibin kudin da take dashi domin ci gaba da gudanar da aikin jin kai a Sudan.
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 18, 2016 04:11 UTC
  • MDD Ta Damu Kan Rashin Kudin Ayyukan Jin Kai A Sudan

Majalisar dinkin duniya, ta sanar da damuwar ta akan makekin gibin kudin da take dashi domin ci gaba da gudanar da aikin jin kai a Sudan.

Bisa ga tsarin data yi a wannan shekara MDD na bukatar agazawa mutane Miliyan 4,6 wadanda dubbai daga cikin su 'yan gudun hijira Sudan din ne da suka bar kasar sanadin rikice-rikice da kuma karamcin abunci.

A watan jiya MDD, ta mika kukan ta ga duniya inda ta ce tana bukatar a hada mata kudade Dala Miliyan 952 na Amurka, aman har zuwa farkon watan nan kudaden data samu su ne Dala Miliyan 242 da dan kai.

Wannan dai ya sa MDD ta bukaci kasashen duniya dasu kara tallafinsu ga Sudan, wanda rashin samunsa zai iya rage yawan mutanen da ake tallafawa.