Damuwa Kan Rashin Sasantuwar Masu Rikici A Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9814-damuwa_kan_rashin_sasantuwar_masu_rikici_a_sudan
MDD da kungiyar tarayya Afrika sun nuna matukar damuwarsu akan rashin sasantuwar bangarorin dake rikici a Sudan domin kawo karshen rikicin a jihohi uku na kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 18, 2016 06:42 UTC
  • Damuwa Kan Rashin Sasantuwar Masu Rikici A Sudan

MDD da kungiyar tarayya Afrika sun nuna matukar damuwarsu akan rashin sasantuwar bangarorin dake rikici a Sudan domin kawo karshen rikicin a jihohi uku na kasar.

Jihohin da rikicin kabilanci yaki ci yaki cinyewa a wannan kasa ta Sudan sun hada da Darfour, Blu-Nile da Kordofan ta kudu.

A mokon daya gabata ne aka yi zamen tattaunawa a Addis Abeba na kasar Habasha da nifin sasanta 'yan tawaye da gwamnatin Sudan domin kawo karshen rikici a yankunan, saidai aka watse a taron ba tare da cimma wata matsaya ba.

Dubban mutane ne dai suka rasa rayukan su kana wasu milyoyi suka yi kaura daga wadannan yankuna domin tsira da rayukansu.