Jan kunan Mataimakin Sudan ta Kudu ga Riek Machar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9832-jan_kunan_mataimakin_sudan_ta_kudu_ga_riek_machar
Sabon Mataimakin Shugaban Sudan ta kudu ya galgadi Madugun 'yan tawayen kasar da ya bar kasar ta zauna lafiya
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 19, 2016 00:50 UTC
  • Jan kunan Mataimakin Sudan ta Kudu ga Riek Machar

Sabon Mataimakin Shugaban Sudan ta kudu ya galgadi Madugun 'yan tawayen kasar da ya bar kasar ta zauna lafiya

A wani jawabi da ya gabatar, sabon Mataimakin Shugaban kasar Sudan ta kudu Taban Deng Gai ya ce wajibi ne tsohon mataimakin shugaban kasar kuma madugun 'yan tawaye Riek Machar da ya fitar da hanunsa daga harakokin siyasar kasar domin a samu sulhu da konciyar hankali a tsakanin Al'umma.

Har ila yau Taban Deng Gai ya bukaci Riek Machar dake a matsayin mai gidansa a baya da ya dauki darasi a kan kura kuran da ya yi a baya.

har ila yau sabon Mataimakin shugaban kasar sudan ta kudun ya kara da cewa idan Riek Machar yana ganin ba zai iya gudanar da rayuwarsa cikin konciyar hankali a kasar ba to yana iya zuwa kasar Kenya ko kuma wata kasa daga cikin kasashen  Afirka ya zuna a can ya kuma jira zaben 2018 domin tsayawa takara a kasar

A shekarar 2013 ne shugaba Salva Keir na  Sudan ta kudu ya zarki mataimakin sa  Riek Machar da yunkurin juyin milki, bayan sauke sa daga kan mikaminsa, a cikin watan Decemba na wannan shekara, Riek Machar ya shiryawa Gwamnatin kasar tawaye, lamarin da ya rikide zuwa yakin cikin gida tsakanin Sojojin dake biyayya ga Gwamnatin Shugaba Salva keir da tsohon mataimakinsa kuma madugun 'yan tawaye Riek Machar.
A cikin watan Augustan 2015,an cimma yarjejjeniyar sulhu tsakanin bangarorin biyu, labarin da ya baiwa Riek Machar damar komawa kan matsayinsa na Mataimakin shugaban kasa, kuma aka sake raba mikaman Gwamnati tsakanin bangaren shugaba Salva da Riek Machar, amma duk da hakan bai yi tasiri ba wajen tabbatar da sulhu ga Al'ummar kasar Sudan ta kudun.

A yayin kusantowar ranar da kasar ke cika shekaru biyar da samun 'yancin kai, a farkon watan Yuli , rikici ya sake barkewa a Juba babban birnin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar sake saukar Riek Machar daga kan mikaminsa na mataimakin shugaban kasa.A irin wannan yanayi wasu na dora Ayar tambaya shin a kwai fatan samun sulhu da konciyar hankali a Sudan ta kudu kuwa nan gaba?

A yayin zaman kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Babban saktare Janar na Majalisar ya baiwa Kwamitin zabi guda uku a kan kasar Sudan ta Kudu, takunkumin sayan makamai, takunkumin bulaguro da kuma na dauka kudade a bankuna  ga wasu daga Shugabanin kasar, ko kuma tura Dakaru 12000 domin karfafa Dakarun wanzar da zaman lafiya dake cikin kasar kuma hakan zai basu damar kare lafiyar fararen hula ko da ma wani sabon rikicin ya barke, wannan zabi na uku shi ne manbobin kwamitin tsaron suka amince da shi.

A halin da ake ciki masu kai Agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun yi galgadi kan halin da 'yan gudun hijra na kasar Sudan ta kudu ke ciki a kasar Uganda, kimanin 'yan Sudan ta kudu dubu 200 ne suka gudu zuwa kasar Uganda a yayin farkewar rikicin baya bayan nan na birnin Juba inda a halin da ake ciki suke fuskantar matsalar karamcin abinci, tsabtaceccen ruwa sha gami da mahali.

Domin samar da abinci ga 'yan gudun Hijrar na Sudan ta kudu dake kasar Uganda, Majalisar Dinkin Duniya ta ce cikin ko wani wata,tana bukatar kimanin miiyon bakwai na dalar Amurka.