Zaman Taro Kan Yaki Da Ta’addanci A Kasar Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9838-zaman_taro_kan_yaki_da_ta’addanci_a_kasar_sudan
An bude wani zaman taro na kasa da kasa a jiya a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan da zimmar ganin an kara samun wayewar kai dangane da batun ta’addanci.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Aug 19, 2016 01:20 UTC
  • Zaman Taro Kan Yaki Da Ta’addanci A Kasar Sudan

An bude wani zaman taro na kasa da kasa a jiya a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan da zimmar ganin an kara samun wayewar kai dangane da batun ta’addanci.

Kamfanin dilalncin labaran kasa Sudan ya bayar da rahoton cewa, wananan taro ya hada bangarori na kasa da kasa gami da ministocin yada labarai na wasu daga cikin kasashen larabawa, inda za a tattauna kan batun fada da ta'addanci.

Fauzi Alghawil shi ne babban darakta na kwamitin hulda da jama’a da yada labarai na kungiyar kasashen larabawa ya bayayna cewa, suna da burin ganin abubuwan da za a tattauna a wannan taro su yi tasiri a cikin kasashen larabawa wajen dakile yan ta’adda da suka addabi al’umma a wannan lokaci.

Sai dai wasu daga cikin masana da suke halartar taron suna ganin cewa, babbar hanyar yaki da ta’addanci ba amfani da makami ba ne kawai, domin ko an kashae ‘yan ta’adda matukar dai akidar ta’addanci tana nan a cikin wasu littafai da kuma fatawoyin wasu malamai masu halasta ayyukan ta’addanci da sunan jihadi, inda suke ganin babu yadda za a iya shawo kan wannan matsala, matukar dai ba a yaki asalin akidar ta'addanci ba, ta hanyar wayar da kai, da canja manhajojin karantarwa a kasashen larabawan da wannan akida ta kafirta musulmi ta yi katutu.