Shugaban 'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Ya Isa Jamhuriyar Dimukradiyar Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9841-shugaban_'yan_tawayen_sudan_ta_kudu_ya_isa_jamhuriyar_dimukradiyar_congo
Jagoran 'yan tawayen Sudan ta kudu Reick Machar ya isa Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, bayan da ya bar kasar Sudan ta kudu sakamakon rikicin da ya kunno kai a tsakaninsa da shugaban kasar Salva Kiir.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Aug 19, 2016 01:21 UTC
  • Shugaban 'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Ya Isa Jamhuriyar Dimukradiyar Congo

Jagoran 'yan tawayen Sudan ta kudu Reick Machar ya isa Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, bayan da ya bar kasar Sudan ta kudu sakamakon rikicin da ya kunno kai a tsakaninsa da shugaban kasar Salva Kiir.

Kakakin majalisar dinkin duniya Farhan Haq ya bayyana cewa, Reick Machar ya isa Congo tun a ranar Laraba da ta gabata, amma a halin yanzu ba su san inda yake da zama a cikin kasar.

Tun kafin wannan lokacin dai mahukuntan kasar Congo sun bukaci majalisar dinkin duniya da ta taimaka wajen ficewar Machar da iyalansa daga kasar Sudan ta kudu zuwa jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, domin samun mafaka ta siyasa.

A ranakun 8 zuwa 11 ga watan Yulin da ya gabata ne dai aka yi bata kashi tsakanin magoya bayan Salva Kiir da kuma Reick Machar, bayan da magoya bayan Machar suka zargi gwamnatin kasar da yunkurin halaka shi, duk da yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin bangarorin biyu.