Congo : Kotu Taki Bada Belin Janar Makoko
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9850-congo_kotu_taki_bada_belin_janar_makoko
Wata Kotu a Brazaville babban birnin kasar Congo tayi wasti da bukatar sakin talala ga janar Jean-Marie Michel Mokoko, dan takara daya sha kaye a zaben shugaban kasar na 20 ga watan Maris.
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 19, 2016 04:04 UTC
  • Congo : Kotu Taki Bada Belin Janar Makoko

Wata Kotu a Brazaville babban birnin kasar Congo tayi wasti da bukatar sakin talala ga janar Jean-Marie Michel Mokoko, dan takara daya sha kaye a zaben shugaban kasar na 20 ga watan Maris.

A watan Yuli ne aka tsare Janar Makoko bisa tuhumarsa da laifin tada zaune tsaye a kasar, da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Saidai lauyoyin dake kare Janar Mokoko din sun ce basu gamsu da hukuncin kotun ba.

Janar Makoko wanda shi ne tsohon hafsan sojin kasar Congo a 1987 zuwa 1993 ya musunta duk wadanan zarge-zargen.