Jamhuriyar Demokradiyyar Congo: An Saki Fursunonin Siyasa
Ministan Shari'a na kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya Sanar da Sakin Fursunonin siyasa 24 daga gidan kurkuku.
Ministan Shari'a na kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya Sanar da Sakin Fursunonin siyasa 24 daga gidan kurkuku.
Kamfanin Dillancin Labrun Reuters ya ambato ministan shari'ar kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo; Alexis Tambowi yana fada a jiya juma'a cewa; Gwamnatin kasar ta dauki matakin watsi da tuhumar da ake yi wa fursunonin siyasar, saboda haka za a saki 24 daga cikin fursunoni 26 da ake tsare da su.
Tun da fari, 'yan hamayyar siyasar kasar sun kafa sharadin sakin fursunonin kafin su zauna kan teburin tattaunawa da shugaban kasa Joseph Kabila akan zaben shugaban kasa da za a yi a anan gaba.
A cikin watan Nuwamba na wannan shekara ta 2016 ne dai za a yi zaben shugaban kasa a kasar ta Jamhuriyar Demikradiyyar Congo.