Harin Ta'addanci Ya Kashe Mutum Guda A Babban Birnin Kasar Somaliya
Harin Bom A Birnin Magadishu Ya ci ran mutum guda
"Yan sandan kasar Somaliya sun sanar da mutuwar mutum guda sanadiyyar tashin wata mota mai makare da bama-bamai a birnin Magadishu.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa daga birnin Magadishu, ya ambato wani jami'in 'yan sandan kasar ta Somaliya, Ibrahim Muhammad yana cewa; Ja'mi'an tsaro suna bin bayan wata mota wacce aka makare da bama-bamai, sai dai ta tarwatse a wani sha-tale-tale a cikin birnin Magadishu,inda ta kashe mutum guda da kuma jikkata wasu hudu.
Jami'in 'yan sandan ya ci gaba da cewa; manufar 'yan ta'addar shi ne kai hari a wani wuri wanda zai shafi fararen hula, sai dai kokarin da jami'an tsaron su ka yi ya dakile manufarsu.
Babu wata kungiya da ta dauki yunkurin kai harin na jiya juma'a, sai dai an fi danganta shi da kungiyar al-shabab.