Tsageran Niger Delta Sun Sake Fasasa Bututu na Mai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9919-tsageran_niger_delta_sun_sake_fasasa_bututu_na_mai
Rahotanni daga yankin Niger Delta dake Tarayyar Nigeria na cewa wasu ‘yan tsagera a yankin sun sake fasa bututun man fetur har biyu a yankin na su.
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 21, 2016 01:18 UTC
  • Tsageran Niger Delta Sun Sake Fasasa Bututu na Mai

Rahotanni daga yankin Niger Delta dake Tarayyar Nigeria na cewa wasu ‘yan tsagera a yankin sun sake fasa bututun man fetur har biyu a yankin na su.

Jami'an Tsaro sun tabbatarwa kamfanin Dillancin labaran kasar Faransa AFP cewa ana ganin aikin ‘yan kungiyar Niger Delta Avengers ne wato NDA a takaice dake nemawa yankin ‘yancin cin gashin kai.

Wani rahoton na cewa an sake samun wata sabuwar kungiyar ‘yan tsagera da ta kunno kai a yankin mai suna Niger Delta Greenland Justice Mandate, NDGJM a takaice.

Majiyoyin na cewa kwanaki uku da suka gabata aka kafa wannan sabuwar kungiya karkashi wani mai suna Aldo Agbalaja da aka fi sani da General.

har ila yau Kungiyoyin dake fafutukan nemawa yankin Niger Delta ‘yanci sun ce a ranar daya ga wata mai kamawa  za su sanar dakafa kasarsu ta kansu.

Baya ga faduwar farashin danyan man a Kasuwanin Duniya, Hare-haren da 'yan tsagerun Niger-Delta ke kaiwa kan bututun Man a Kasar ya janyo kalu bale ga tattalin arzikin kasar, inda a halin dake ciki kasar ta shiga cikin wani yanayi da ba ta iya biyan albashin Ma'aikata a kan lokaci.