An dake zaben shugaban kasar a D/Kwango
Kwamitin zabe na Jumhoriyar Demokaradiyar Kwango ya dage zaben shugaban kasar har zuwa watan yunin 2017
kamfanin dillancin labaran Reuteus daga birnin Kinshasa ya nakalto Shugaban Hukumar zaben Kasar Kwango a jiya Assabar na cewa rajistar mutane sama da miliyan 30 daga aka fara tun daga watan Maris din da ya gabata yana bukatar lokaci mai tsoho domin a gudanar da aiki mai kyau, bisa nazari da kwararru suka yi sun bukaci watani 16 domin kamala wannan aiki, hakan ya sa muka ya dace a dage zaben har zuwa cikin watan yunin shekara 2017.
Kafin wannan sanarwa kotun kundin tsarin milkin kasar ta sanar da cewa matukar ba a gudanar da zaben shugaban kasar a lokacinsa ba wato a watan Nuwanba mai zuwa ba, to Gwamnatin Shugaba Joseph Kabila na iya ci gaba da jan ragamar jagorancin kasar har zuwa lokacin da za a gudanar da zaben.
Tun a shekarar 2001 ne shugaban Joseph kabila ya gaji ma'aifinsa, a shekarar 2006 aka zabi Joseph kabila a matsayin shugaban kasa karo na farko sannan kuma a shekarar 2011 aka sake zabensa a wa'adi na biyu, bisa dokar kundin tsarin milkin kasar Jumhoriyar Demokaradiyar Kwango,a karshen watan Decemba ne ya kamata Shugaba kabila ya sauka daga kan karagar milkin kasar, 'yan adawa na zarkin cewa Shugaba Kabila na jan lokacin zaben ne domin karawa kansa lokaci na zama a kan karagar milki.