Somaliya : Harin Al'Shabab Ya Kashe Mutane 10
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9934-somaliya_harin_al'shabab_ya_kashe_mutane_10
'Yan sanda a Somliya sun sanar da mutuwar mutane goma sakamakon wasu jerin hare hare bom a birnin Galkayo dake tsakiyar kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:48+00:00 )
Aug 21, 2016 06:40 UTC
  • Somaliya : Harin Al'Shabab Ya Kashe Mutane 10

'Yan sanda a Somliya sun sanar da mutuwar mutane goma sakamakon wasu jerin hare hare bom a birnin Galkayo dake tsakiyar kasar.

An dai kai harin ne da motoci biyu a harabar fadar gwamnatin yankin.

An dai kai harin na farko ne da wata motar dakon mai, yayin da na biyu aka kaisa da motar daukan fassinja.

tuni dai kungiyar Al'shabab ta dauki alhakin kai harin a manhajar ta ta Telegram tare da cewa ta kashe mutane kimanin 30 ciki har da sojoji.