Sabon Mataimakin Sudan Ta Kudu Ya Fara Ziyarar Aiki A Khartum
Mataimakin shugaban kasar Sudan ta kudu Taban Deng Gai ya fara gudanar da wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jamhuriyar Sudan, inda ya isa birnin Khartum a yau.
Karamin ministan harkokin waje na kasa Sudan Kamaluddin Isma'il ya fadi yau cewa, Taban Deng zai gana da manyan jami'an gwamnatin Sudan da suka hada da shugaba Umar Hassan Albashir, a kan batutuwa da suka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu.
Shugaban kasar Sudan ta kudu ya nada Taban Deng Gai a matsayin mataimakinsa ne biyo bayan rikciin da ya barke tsakanin magoya bayansa da kuma magoya bayan Reik Machar madugun 'yan tawaye, wanda ya dawo Juba a matsayin mataimakin shugaban kasa bayan yarjejeniyar sulhu da aka cimmawa, sai kungiyar kasashen gabashin Afirka IGAD ta ce ba ta amince da nada Taban Deng a matsayin mataimakin shugaban kasar Sudan ta kudu ba.