-
An Kashe 'Yar Majalisar Dokokin Kasar Somaliya
Mar 29, 2018 01:06Wasu 'yan bindiga sun bindige wata 'yar Majalisar dokokin kasar Somaliya a Magadushu babbar birnin kasar
-
'Yan Sandan Nijeriya Sun Ce Suna Neman Sanata Dino Melaye Ruwa A Jallo
Mar 28, 2018 11:42Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta sanar da cewar tana neman Sanata Dino Melaye, dan majalisar tarayya daga jihar Kogi tare da dan tsohon gwamnan jihar Kogin Muhammad Audu saboda zarginsu da ake yi da ba da bayanan karya ga 'yan sanda.
-
Dubban 'Yan Kasar Ghana Na Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Jibge Sojojin Amurka A Kasar
Mar 28, 2018 11:41Dubun dubatan al'ummar kasar Ghana ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin Accra, babban birnin kasar, don nuna rashin amincewarsu da yarjejeniyar fadada alaka ta soji tsakanin kasar Ghanan da kasar Amurka lamarin da zai ba wa Amurkan damar jibge sojojinta a kasar Ghanan.
-
'Yan Adawan Chadi Suna Zargin Shugaba Derby Da Kafa Mulkin Mulukiya A Kasar
Mar 28, 2018 11:41Rahotanni daga kasar Chadi na nuni da cewa ana shirin kafa dokar da za ta ba wa shugaban kasar Idris Derby damar ci gaba da mulkin kasar har zuwa shekara ta 2033 da kuma ba shi karfin iko mai girman gaske lamarin da 'yan adawa a kasar suka ce wani kokari ne na mai da kasar karkashin tsari na mulukiya.
-
'Yan Majalisar Zambiya Sun Jinkirta Kada Kuri'ar Tsige Shugaban Kasar
Mar 28, 2018 11:41'Yan majalisar kasar Zambiya sun jinkirta tattaunawar da kuma kada kuri'ar da aka shirya za a gudanar a yau din nan Laraba kan daftarin kudurin da aka gabatar na tsige shugaban kasar Edgar Lungu bisa zargin yin karen tsaye ga kundin tsarin mulkin kasar.
-
Jami'an Tsaron Tanzaniya Sun Kama Madugun 'Yan Adawar Kasar
Mar 28, 2018 08:11Ma'aikatar shari'ar Tanzaniya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun kame madugun 'yan adawar Tanzaniya.
-
Al'ummar Masar Suna Ci Gaba Da Kada Kuri'ar Zaben Shugaban Kasa A Rana Ta Karshe
Mar 28, 2018 08:06Al'ummar Masar suna ci gaba da kada kuri'a a ranar karshe ta zaben shugaban kasa a yau Laraba.
-
Gwamnatin Mali Ta Jaddada Aniyarta Ta Yaki Da Ayyukan Ta'addanci A Kasar
Mar 28, 2018 08:03Fira ministan Mali ya bukaci hadin kan kasa a Mali tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da ayyukan ta'addanci a kasar.
-
Burkina Faso: Fiye Da Mutane Dubu Biyar Sun Zama 'Yan Gudun Hijira
Mar 28, 2018 04:57Kungiyar Agaji ta Red cross ta ce mutanen da ke yankin arewacin kasar ta Burkina Faso sun yi hijira ne domin kaucewa hare-haren masu akidar "takfiriyyah'
-
An Sanar Da Sabon Fira Ministan Kasar Habasha
Mar 28, 2018 04:53A jiya talata ne kawancen jam'iyyun da ke mulki a kasar ta Habash ya sanar da sunan Abiye Ahmed a matsayin wanda zai maye gurbin Hailemarim Desalegn da ya yi murabus.