-
Dakarun Somaliya Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Kungiyar Al-Shabab Su Bakwai
Mar 15, 2018 07:50Sojojin kasar Somaliya sun sami nasarar hallaka wasu 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab ta kasar su bakwai a wani hari da suka kai musu a garin bakin ruwan nan na Kismayo da ke kudancin kasar.
-
Kokarin Gwamnatin Najeriya Na Ceto 'Yan Matan Dapchi
Mar 15, 2018 03:42Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirinta na ceto 'yan matan sakanderen Dapchi da mayakan boko haram suka yi awan gaba da su cikin watan da ya gabata.
-
Shugaba Buhari Ya Gana Da Iyayen 'Yan Matan Dapchi Da Aka Sace
Mar 15, 2018 02:08Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gana da iyayen 'yan matan sakandaren Dapchi da mayakan kungiyar Boko Haram suka sace a kwanakin baya.
-
Kenya: Za A Kafa Wata Cibiyar Musulunci Domin Dakile Yaduwa Tsatsauran Ra’ayi
Mar 15, 2018 02:08Musulmin kasar Kenya na shirin gina wata cibiyar musulunci wadda za ta mayar da hankali wajen fada da tsatsauran ra’ayin addini a kasar.
-
Gwamnatin Najeriya Ba Za Ta Yi Kasa A Guiwa Ba Har Zuwa Sako 'Yan Matan Dapchi
Mar 14, 2018 15:38Shugaban kasar ta Najeriya Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka a yayin da ya ziyarci Jahar Yobe, yana mai cewa sai an saki dukkanin 'yan matan Chibok da Dapchi
-
Libya: "Yan Ci-Rani 119 Sun Tsira Daga Cin Ruwa
Mar 14, 2018 15:37Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato kakakin sojojin ruwan Libya, Ayuba Kasim yana sanar da ceto 'yan ci-ranin 119 a yau Laraba
-
Hukumar Zaben Saliyo Ta Sanar Da Ranar Gudanar Da Zagaye Na Biyu Na Zaben Shugaban Kasar
Mar 14, 2018 07:36Hukumar zaben kasar Saliyo ta tsayar da ranar 27 ga watan Maris na da muke ciki a matsayin ranar da za a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar bayan da ta sanar da sakamakon karshe na zagayen farko na zaben da aka gudanar a ranar 7 ga watan Maris inda babu dan takarar da ya sami kuri'un da ake bukata na ya lashe zaben a zagayen farko.
-
Kokarin Ganin Shugaban Burundi Ya Ci Gaba Da Zama A Kan Karagar Mulkin Kasar
Mar 14, 2018 03:00Jam'iyya mai mulki a Burundi ta bukaci gudanar da zaben raba gardama domin bada dama ga shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2034.
-
Matsalar Rashin Aikin Yi Musamman A Tsakanin Matasa A Kasar Moroko
Mar 14, 2018 02:58Tashar talabijin ta France 24 ta bada labarin cewa: Matsalar rashin aikin yi a Moroko ta yi kamari musamman a tsakanin matasan kasar.
-
Wasu Mahara Sun Kashe Jami'an Jamdarma 3 A Nijer
Mar 13, 2018 15:33Wasu mahara kan babura sun kai hari kan jami'an tsaron Jandarma na Nijer a karamar hukumar Ouallam na jahar Tilabery tare da kashe uku daga cikinsu