Libya: "Yan Ci-Rani 119 Sun Tsira Daga Cin Ruwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29077-libya_yan_ci_rani_119_sun_tsira_daga_cin_ruwa
Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato kakakin sojojin ruwan Libya, Ayuba Kasim yana sanar da ceto 'yan ci-ranin 119 a yau Laraba
(last modified 2018-08-22T11:31:33+00:00 )
Mar 14, 2018 19:07 UTC
  • Libya:

Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato kakakin sojojin ruwan Libya, Ayuba Kasim yana sanar da ceto 'yan ci-ranin 119 a yau Laraba

AYub Kasim ya kara da cewa; Tuni an dauki Mutanen 119 zuwa sansanin da ke yankin Tajurah a kusa da birnin Tripoli, babban birnin kasar.

Wata kididdiga ta hukumar kasar Libya ta ambaci cewa daga farkon watan Maris zuwa yanzu an tseratar da mutane 6000 daga nutsewa a ruwa.

Kasar Libya yanya ce mai muhimmanci ta 'yan ci-rani masu son shiga turai.

Masu fasakwaurain mutane suna amfani da rashin tsaron da ake da shi a kasar Libya domin jigilar masu son shiga kasashen turai ta hanyar da ba ta dace ba.

A shekarar  2017 da ta gabata dubban yan ci-rani daga nahiyar Afirka ne su ka halaka acikin ruwan kasar Libya.