Iran Ta Yi Watsi Da Zargin Aika Makamai Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i10175-iran_ta_yi_watsi_da_zargin_aika_makamai_yemen
Ministan Harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif ya yi watsi da zargin takwaransa na Amurka John Kerry na cewa, Iran ta aike makaman yaki a kasar Yemen.
(last modified 2018-08-22T06:58:49+00:00 )
Aug 26, 2016 09:26 UTC
  • Iran Ta Yi Watsi Da Zargin Aika Makamai Yemen

Ministan Harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif ya yi watsi da zargin takwaransa na Amurka John Kerry na cewa, Iran ta aike makaman yaki a kasar Yemen.

Mr Zarif na maida martani ne kan zargin Kerry na cewa Iran ta aike da makaman yaki a Yemen, inda ya kara da cewa wannan zance ne mara tushe na kiyaya ga Iran.

Mr Zarif ya kara da cewa Kerry ya fi kowa sannin irin take hakkin bil adama da laifukan yaki da Saudiyya ke aikatawa a Yemen a tsawan wattani 18 da kuma yin kafar ungulu da duk wani yunkuri kawo karshen yakin a Yemen, aman babu wani abu data yi na tsawatawa kawarta.

Hakazalika Mr Zarif ya bukaci Amurka data bude idannunta ta kuma dauki darasi daga abunda ke ci gaba da faruwa a kasashen Siriya da Iraki, wanda shi Kerry din ya fi kowa sanin tushensa, kuma kasarsa Amurka tana ci gaba da rufe idannu a kai.