Iraniyawa Miliyan Daya Sun Isa Iraqi
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Iraki ta sanar da cewa Iraniyawa miliyan daya sun shiga kasar domin ziyara
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Iraki ta sanar da cewa Iraniyawa miliyan daya sun shiga kasar domin ziyara.
Babban jami'i mai kula da iyakokin kasar Iraki, Samy Sudany, ya fadawa tashar telbijin din Press tv a jiya laraba cewa; Iraniyawa miliyan daya sun isa kasar domin karanta ziyarar Arfah.
Al-Sudany ya ci gaba da cewa; Ta hanyar kasa guda daya, wato Zarbadiyah-Mehran, da ke gabacin kasar Iraki, Iraniyawa miliyan daya ne su ka shiga.
Jami'in ya kara da cewa; Ashekarar bana, Iraniyawan za su karanta ziyarar Arfah a hubbaren Imam Husaini da Abul-Fadl ( a.s).
Bayan da mahukuntan Saudiyya su ka hana Iraniyawa zuwa aikin haji a bana, da dama sun tafi kasar Iraki domin karanta ziyarar Arfah.