Iran Tayi Maraba Da Shirin Tsagaita Wuta A Syria
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i10882-iran_tayi_maraba_da_shirin_tsagaita_wuta_a_syria
Iran ta ce tana maraba da shirin tsagaita wuta wanda kasashen Amurka da Rasha suka shata.
(last modified 2018-08-22T11:28:54+00:00 )
Sep 11, 2016 10:45 UTC
  • Iran Tayi Maraba Da Shirin Tsagaita Wuta A Syria

Iran ta ce tana maraba da shirin tsagaita wuta wanda kasashen Amurka da Rasha suka shata.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Bahram Ghasemi ya ce Iran tana maraba da wannan yerjejeniya saidai ya kamata a hankara sosai kada 'yan ta'adda suyi amfani da wannan damar.

Hakazalika Iran ta mika fatan  ta na ganin kayan agaji sun isa ga duk wadanda abun ya shafa ba tare da bangaranci ba.

A ranar Juma'a data gabata ce sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da Ministan harkokin waje na Rasha, Sergei Lavrov suka cimma yarjejeniya tsagaita wuta a Geneva wace zata fara aiki gobe Litinin wato ranar babbar Sallah.