Jawabin Barka da Salla na Shugaban Iran ga Kasashen Musulmai
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i10906-jawabin_barka_da_salla_na_shugaban_iran_ga_kasashen_musulmai
Shugaban Jumhoriyar musulinci ta Iran ya gabatar da Jawabin Barka da Salla ga dukkanin Kasashen Musulinci.
(last modified 2018-08-22T11:28:54+00:00 )
Sep 11, 2016 17:22 UTC
  • Jawabin Barka da Salla na Shugaban Iran ga Kasashen Musulmai

Shugaban Jumhoriyar musulinci ta Iran ya gabatar da Jawabin Barka da Salla ga dukkanin Kasashen Musulinci.

A wata sanarwa da fadar Shugaban kasar ta fitar a marecen yau Lahadi, Shugaban Jumhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani ta yiwa daukkanin Al'ummar musulmin Duniya barka da babbar salla.

A cikin sanarwa, Shugaban Kasar Iran ya bayyana kyakkyawan fatansa na ganin cewa Al'ummar musulmi sun yi amfani da wannan dama ta babbar salla, musaman wadanda a..ya basu damar zuwa aiki hajji na bana, da aiki tare wajen bayyana wa Duniya hakikanin Addinin Islama wanda Ma'aikin A...Muhamadu Dan Abdull..tsira da amincin a... su tabbata a gare shi tare da iyalan gidan tsarkaka ya zo da shi wanda yake tattare da Rahama, tausayi  gami da Adalci.

Har ila yau Dakta Rauhani ya bukaci Al'ummar musulmi da su dage wajen tunkarar masu sanya rarrabuwar kawuna a tsakanin su kuma su zamanto masu kaunar juna da tausayi kamar yadda musulincin da Annabi Muhamadu (s.a.w) ya zo da shi.