Ganawar Shugabanin kasashen Iran da Venezuela a birnin Caracas
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i11143-ganawar_shugabanin_kasashen_iran_da_venezuela_a_birnin_caracas
Shugabanin kasashen Iran da Venezuela sun tabbatar da bada gudumuwa wajen tabbatar da sulhu gami da zaman lafiya a Duniya
(last modified 2018-08-22T11:28:56+00:00 )
Sep 17, 2016 05:49 UTC
  • Ganawar Shugabanin kasashen Iran da Venezuela a birnin Caracas

Shugabanin kasashen Iran da Venezuela sun tabbatar da bada gudumuwa wajen tabbatar da sulhu gami da zaman lafiya a Duniya

Kamfanin dillancin Irna na kasar ya habarta cewa a daren jiya Juma'a Shugaban Jumhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani ya gana da takwaransa na kasar Venezuela a birnin Caracas fadar milkin kasar, inda ya taya shi murna da fara shugabanicin kasar sa na kungiyar kasashe 'yan baruwanmu tare da bayyana cewa Tehran a shirye take ta taimakawa Venezuelan da irin kwarewar da take da ita a yayin da take jagorantar kungiyar.

A yayin da yake ishara kan irin sauyi da aka samu a yankin da Duniya baki daya, Shugaba Rauhani ya ce kungiyar na iya taka muhimiyar rawa wajen kawo sauyi a Duniya to saidai hakan ba zai tabbata ba sai da hakin kai tare kuma da aiki tare na manbobin kungiyar.

Yayin da yake ishara kan faduwar farashin Man fetur a Duniya, Shugaban kasar Iran ya tabbatar da cewa samun tabbaci  a Kasuwar danyan Man, daidaita farashin Danyan Man, da kuma kaso na adalci wajen hako  danyan Man, shi zai tabbatar da amfanin masu fitarda Man da kuma masu amfani da shi.

Shugaba Dakta hasan Rauhani ya bayyana fatansa na kara fadada alaka a fanonin daban daban musaman wajen saka hanun Jari tsakanin kasar sa da kasar Venezuela.

A yau Assabar za a bude taron kungiyar kasashen 'yan baruwanmu karo na 17 a tsibirin Margarita na kasar Venezuela, inda shugaban kasar Iran zai meka Jagorancin kungiyar ga Kasar Venezuelan.