Ziyarar Shugaban kasar Iran zuwa kasar Cuba
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i11257-ziyarar_shugaban_kasar_iran_zuwa_kasar_cuba
Shugaban Jumhoriyar musulinci ta Iran ya amsa goron gayyatar takwarsa na Cuba Raul Castro
(last modified 2018-08-22T11:28:57+00:00 )
Sep 19, 2016 17:44 UTC
  • Ziyarar Shugaban kasar Iran zuwa kasar Cuba

Shugaban Jumhoriyar musulinci ta Iran ya amsa goron gayyatar takwarsa na Cuba Raul Castro

Bayan taron kungiyar kasashen 'yan baruwanmu da ya gudana a tsibirin Margarita na kasar Venezuela, Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Raunai ya kama hanya zuwa birnin Havana na kasar Cuba inda ya amsa goron gayyata na takwaransa Raul Castro,manufar wannan ziyara dai fadada alakar dake tsakanin birnin Tehran da birnin Havana.

A yayin Jawabin da ya gabatar a wurin taron Kungiyar kasashen 'yan baruwanmu karo na 17 da ya gudana a tsibirin Margarita na kasar Venezuela, Shugaba Rauhani ya gabatar da rahoton shekaru hudu da kasar sa ta yi tana Jagorantar wannan Kungiya sannan ya meka ragamar jagorancin Kungiyar ga Kasar Venezuela na shekaru uku masu zuwa.

A gefen taron, Shugaban Jumhoriyar musulinci ta Iran ya gana da Shugabani gami da manyan Jami'an kungiyar a kasar Venezuela.

Bayan kasar Cuba Shugaba Rauhani zai isa birnin New York na kasar Amurka domin gudanar da jawabi a taron dake gudana a zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 71.