Airbus Ya Samu Izinin Sayarwa Iran Jiragan Sama
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i11368-airbus_ya_samu_izinin_sayarwa_iran_jiragan_sama
Kanfanin kera jiragen sama na faransa Airbus, ya sanar a wannan Laraba cewa ya samu izinin farko daga Amurka na sayarwa da Iran jiragen sama na fasinja.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 21, 2016 13:55 UTC
  • jirgin fasinja kira Airbus na kanfanin Iranair
    jirgin fasinja kira Airbus na kanfanin Iranair

Kanfanin kera jiragen sama na faransa Airbus, ya sanar a wannan Laraba cewa ya samu izinin farko daga Amurka na sayarwa da Iran jiragen sama na fasinja.

Kanfanin ya ce ya samu izini na farko, aman yana jiran na biyu cikin dan takaitacen lokaci domin shirya sayarwa da Iran jiragen, wanda zai kasance na farko tun bayan dage mata takunkumi.

kakakin kanfanin na Airbus, ya shidawa kanfanin dilancin labarai faransa na AFP cewa sun samu lasisin farko jiya Talata cikin biyu da suka nema wajen Amurka, kuma hakan zai basu damar aiwatar da yerjejeniyar sayarwa da Iran jiragen.

A cewar kanfanin  lasisin zasu bada damar sayarwa da Iran jigarenn jigilar fasinja matsakaita kirar A320 da kuma masu dogon balaguro kirar A330.

A karshen watan Janauru ne jamhuriya musulinci ta Iran da kanfanin na Airbus suka cimma yarjejeniyar da Iran jiragai 118 da suka tasa sabar kudi kusan $ Amurka bilyan 11, saidai kasancewar akwai wani bangare na kayan jiragen da mallakar Amurka ne ana bukatar izininta.