Rohani Ya Gana Da Firaministan Italiya A New-York
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i11374-rohani_ya_gana_da_firaministan_italiya_a_new_york
A ziyara da yake a binbin New York na Amurka inda yake halartar taron koli na MDD karo na 71, shugaban kasar Iran Hassan Rohani na ci gaba da ganawa da shugabanni da mayan jami'an kasashen duniya.
(last modified 2018-08-22T11:28:58+00:00 )
Sep 21, 2016 18:10 UTC
  • Shugaban kasar Iran Hassan Rohani da firaministan Italiya Matteo Renzi
    Shugaban kasar Iran Hassan Rohani da firaministan Italiya Matteo Renzi

A ziyara da yake a binbin New York na Amurka inda yake halartar taron koli na MDD karo na 71, shugaban kasar Iran Hassan Rohani na ci gaba da ganawa da shugabanni da mayan jami'an kasashen duniya.

A wannan laraba shugaba Rohani ya gana a daura  taron da firaministan kasar Italiya Matteo Renzi, inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen biyu.

Kasashen Iran da Italiya dai nada kyakyawar alaka tsakaninsu musamen ta bangaren kasuwanci.

A yayin ganawarsa da Mr Renzi, shugaba Rohani ya bayyana cewa, cimma yarjejeniyar nulikiya da kasarsa tayi da mayan kasashen duniya, ya baiwa Italiya damar zama abokiyar hulda ta farko a fannin kasuwanci a nahiyar Turai.

Shi kuwa a nasa bangare firaministan na Italiya  Matteo Renzi ya bayyana kyakyawan fatansa na ganin kasarsa ta kara karfafa alaka da kasuwanci da Jamhuriya musulinci ta Iran.