Jawabin Jagoran Juyin Musulunci Akan Makon Tsaro
Jagora: Dacen Da Iran ta samu a wannan lokacin tushensa sadaukar da kai na shahidai.
A cikin sakon da ya fitar a yau alhamis dangane da makon tsaro, jagoran juyin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; Dacen da al'ummar Iran su ka samu a wannan lokacin tushensa jagorancin shahidai da wadanda su ka sadaukar da kawukansu.
Sakon na Jagoran juyin musulunci na Iran ya ci gaba da cewa; Rayuwa da mutuwar shahidai ita ce ta bai wa al'ummar musulmi daukaka.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana cewa; Muna godiya ga Allah da cewa a zamaninmu ne ma'anar koli ta shahada ta bayyana kuma zukata masu tsarki su ka zama suna shaukinta.
A jiya laraba ne dai 31 ga watan Shahribar na hijira shamshiyya aka fara makon tsaro, da ya zo daidai da lokacin harin da Saddam na Iraqi ya kawo wa Iran.