Hudubar Sallar Juma'a A Birnin Tehran Fadar Mulkin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Karfin da sojojin kasar Iran suke da shi ya kara janyo samuwar zaman lafiya da tsaro a yankin gabas ta tsakiya.
A hudubar sallar Juma'arsa ta yau a babban Masallacin birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran: Hujjatul-Islam Kazim Siddiqi ya tabo batun kallafaffen yakin shekaru takwas da al'ummar Iran suka yi da gwamnatin Ba'as ta Iraki: Yana mai fayyace cewa; Kallafaffen yakin ya nuna matsayin jarumtaka da gagarumar nasarar da juyin juya halin Musulunci ya yi a kan manyan kasashe masu girman kai a duniya.
Hujjatul-Islam Sadiqi ya kara da cewa: Tsawon shekaru takwas al'ummar Iran suka yi suna kare kansu daga zaluncin manyan kasashen duniya masu girman kai, kuma tarihi ya tabbatar da cewa; Al'ummar Iran ba mutane ne masu nuna fin karfi ko wuce gona da iri kan wata al'umma ba, amma a shirye suke su kare kansu daga duk wani gigin wuce gona da iri kan kasarsu ta hanyar mai da martani mai gauni.