Duniyar Musulunci Na Bukatar Hadin Kai
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i11488-duniyar_musulunci_na_bukatar_hadin_kai
Hadin Kai A duniyar musulunci ya zama wajibi
(last modified 2018-08-22T11:28:58+00:00 )
Sep 24, 2016 08:23 UTC
  • Duniyar Musulunci Na Bukatar Hadin Kai

Hadin Kai A duniyar musulunci ya zama wajibi

Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Kasar Turkiya ya ce; Duniyar musulunci tana da bukatuwa da hadin kai

Muhammad Ibrahim Tahiriyan Fard, da ya gana da shugaban kungiyar addinai ta kasar Turkiya Muhammad Gurmuz, ya  kuma yi ishara da juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Turkiya sannan ya kara da cewa; Tun a farkon juyin mulkin ne, Jamhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana kasantuwarta tare da gwamnati da kuma al'ummar kasar ta Turkiya.

A nashi gefen Muhammad Gurmuz ya bayyana cikakken fatansa na ci gaba da bunkasar alaka a tsakanin kasashen biyu.