Shugaban Majalisar kasar Kenya ya gana da Ministan Man na kasar Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i11563-shugaban_majalisar_kasar_kenya_ya_gana_da_ministan_man_na_kasar_iran
Ministan Man kasar Iran ya ce a halin yanzu a samu yanayi mai kyau na bunkasa alaka tsakanin kasashen Iran da Kenya
(last modified 2018-08-22T06:58:59+00:00 )
Sep 25, 2016 14:52 UTC
  • Shugaban Majalisar kasar Kenya ya gana da Ministan Man na kasar Iran

Ministan Man kasar Iran ya ce a halin yanzu a samu yanayi mai kyau na bunkasa alaka tsakanin kasashen Iran da Kenya

A wannan lahadi Ministan Man fetur na Jumhoriyar musulinci ta Iran Bijan Zanganeh ya gana da Shugaban Majalisar dokokin kasar Kenya Justin motor Adnan a nan birnin Tehran, a yayin ganawar ta su ministan Man na Iran ya bayyana cewa tun da a dage takumkumin zalincin da aka kakabawa kasar sa to yanzu an samu yanayi mai kyau na bunkasa alaka tsakanin kasashen Iran da Kenya, kuma kasashen biyu na iya bunkasa alakar su a bangarori daban daban musaman ma a bangaren musayar Man fetur  tsakanin kasashen biyu.

Har ila Zangeneh ya ce a baya a kwai yarjejjeniya da aka cimma tsakanin kasarsa da kenya amma saboda matsalar takunkumi ba a iya zartar da dukkanin su ba, amma a yanzu kasashen biyu na da damar zartar da su ba tare da wata matsala, kuma kyautata alaka da kasashen Afirka na daga cikin siyasar da kasar sa ta fi fifitawa a harakokin siyasar ta na kasashen waje.

A nasa bangare Shugaban Majalisar Dokokin na kasar Kenya ya tabbatar da cewa kasar sa za ta bunkasa alakar ta da kasar Iran a bangarorin daban daban,a na sa ran shugaban Majalisar kasar ta kenya zai gana da takwaransa na Jumhoriyar musulinci ta Iran Ali Larijani.