Bama Shirye, Don Cimma Yarjejeniyar Takaita Fitar Da Man Fetur, Inji Iran
Iran ta ce ba a shirye take ba don cimma yarjejeniya a Aljeriya don takaita fitar da man fetur din da take samarwa domin farfado da farashinsa a duniya.
Ministan man fetur din kasar ne kasar Bijan Namdar Zanganeh ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wannan Talata, inda yake cewa, cimma yarjejeniya kan wannan batu cikin kwana biyu baya daga cikin ajandar kasar.
Mista Zanganeh, ya kara da cewa kasar na bukatar lokaci don kara tuntuba, aman ya ce za'a iya cimma jarjejeniya kan wannan batun a yayin taron kungiyar kasashen masu arzikin man fatur na OPEP da zai gudana a ranar 30 ga watan Nuwamba mai zuwa a Vienna.
Iran dai ta ce tana bukatar habaka man da take fitarwa zuwa ganga miliyan hudu a rana, maimakon miliyan 3,6 zuwa 3,8 da take fitarwa ko wace rana a yanzu.