Jagora: Dolene Sojojin Kasar Iran Su Sami Kwarewar Kare Kasar
Jagoran juyinn juya halin musulunci a nan Iran Ayatullah Sayyid Aliy Khamenei ya bayyana cewa dole ne sojojin kasar Iran su kasance suna da korewa da kuma karfin kare kasar daga baranar makiya a ko da yauce.
Jagoran ya bayyana haka ne a yau Laraba a lokacinda yake halattar bukin yaye sojojin a makarantar sojoji ta Imam Husain (a) dake nan Tehran. Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana cewa " a halin yanzu kasar Iran tana fuskantar baraza daga bangarori da dama don irin matsayin da ta dauka na kare addinin musulunci da kuma kasancewa 'yentacciyar kasa a duniya. Don haka sojojin kasar dole ne su kasance cikin shirin aiwatar da abinda ya hau kansu a dok lokacinda bukatar haka ta taso.
Ayatollah Khamenei ya ce yakin shekaru 8 wanda sojojin kasar suka tabka da sojojin kasar Iraqi ya zama wani dame na nuna kwarewa da kuma gogewa a harkokin yaki ga sojojin kasar don haka bai kamata su manta da wannan korrewar ba musaman a lokacinda kasar take fuskantar barazana daga bangarori daban daban a duniya.