Taron Kwamitin Hadin Gwiwa Na Kasashen Iran Da Afirka ta Kudu.
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i11785-taron_kwamitin_hadin_gwiwa_na_kasashen_iran_da_afirka_ta_kudu.
Taron Bunkasa Alaka A tsakanin Iran Da Afirka ta kudu
(last modified 2018-08-22T06:59:00+00:00 )
Sep 30, 2016 15:30 UTC
  • Taron Kwamitin Hadin Gwiwa Na Kasashen Iran Da Afirka ta Kudu.

Taron Bunkasa Alaka A tsakanin Iran Da Afirka ta kudu

Kwamitn Hadin gwiwa a tsakanin Iran da Afirka ta kudu, ya  bude taronsa karo na bakwai a Pretoria.

Jami'i mai kula da alakar Iran da kasashen Larabawa da Afirka, a ma'aikatar harkokin  waje, Husain Jabiry Ansary, ya tattauna da jami'an kasar Afirka ta kudu a jiya alhamis, dangane da yarjejeniyoyin da aka kulla a baya.

Taron ya maida hankali ne akan bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu a fagagen man fetur da tsaro da fada da ta'addanci.

Bugu da kari, jami'in na ma'aikatar harkokin wajen Iran, ya jaddada muhimmacin yin amfani da siyasa wajen warware matsalar kasar Syria.

Duk bayan watanni 6 ne kwamitin ya ke yin taronsa a tsakanin Afirka ta kudu da kuma Iran.