Bunkasa Alakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Kasashen Iran A Malayzia
A ziyarar aiki da shugaba Hassan Rauhani na kasar Iran ya kai kasar Malayzia a ziyarar aikin da yake yi a kasashen nahiyar Asia, an rattaba hannu kan kara bunkasa alakar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen Iran da Malayzia.
A lokacin da suke gudanar da taron manema labarai a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malayzia, shugaba Rauhani tare da Firayi ministan kasar Malayzia, sun sanar da rattaba hannu kan kara bunkasa alaka a dukkanin bangarori na tattalin arziki da cinikayya da hada-hadar kudade a tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Rauhani ya bayyana kasashen Iran da Malayzia a matsayin amnyan kasashe biyu na musulmi da suka nisa ta fuskar kimiyya da fasa da kuma kere-kere, tare da bayyana aiki tare a tsakanin kasashen zai amfanar da al'ummominsu matuka da ma al'ummar musulmi.
Shi ma a nasa bangaren Firayi ministan kasar ta Malayzia Muhammad najib Razzaq ya bayyana ziyarar ta shugaba Rauhani da cewa tana da matukar muhimmanci ga kasarsa, domin ta kara bayar da dama wajen tattauna batutuwa da suke da matukar alfanu ga dukkanin bangarorin biyu, musamamn ma batun saka hannayen jari na kamfanonin Malayzia a Iran, wanda an riga an cimma matsaya a kansa a yayin wannan ziyara ta shugaba Rauhani.