Rohani Ya Halarci Taron Ashura A Kudancin Tehran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i12367-rohani_ya_halarci_taron_ashura_a_kudancin_tehran
Shugaban Iran Hassan Rohani, wanda ya halarci taron juyayin Ashura a kudancin Tehran babban birnin kasar, ya yi fata ga al'ummar Syria, Iraki da kuma Yemen na ganin su kawar da kungiyoyi na masu tada kayar baya da kuma 'yan ta'adda.
(last modified 2018-08-22T11:29:04+00:00 )
Oct 12, 2016 16:59 UTC
  • Rohani Ya Halarci Taron Ashura A Kudancin Tehran

Shugaban Iran Hassan Rohani, wanda ya halarci taron juyayin Ashura a kudancin Tehran babban birnin kasar, ya yi fata ga al'ummar Syria, Iraki da kuma Yemen na ganin su kawar da kungiyoyi na masu tada kayar baya da kuma 'yan ta'adda.

Mista Rohani wanda ya halarci taron na Ashura a yankin Hazrat-el Abdul Azim Al-Hassan, ya kuma ce a bana al'ummar Iran sun fito dafifi fiye da bara domin jaddada biyayarsu ga jikan Mazon Allah (SAW).  

Rohani ya kara da cewa samun alhairi anan duniya da kuma gobe kiyama yana ga koyi da da koyarwa ta Iman Hossein (AS).

A yayin da yake masa tambayoyi ga manema labarai, Shugaba Rohani ya yi fatan ganin al'ummar Yemen da rayuwa a cikin hare-haren zalunci, da kuma na Syria da fama da hare-haren 'yan ta'adda masu kafirta musulmi da yardar Allah zasu murkushe wadanan kungiyoyi.

kamar sauran al'ummar musulmi shi'a, a yau ne milyoyin Iraniyawa suka gudanar da tarurukan juyayin Ashura, kuma har kawo yanzu babu wani tashin hankali ko barazana ko makamancin hakan da aka fuskanta a duk fadin kasar, illah kawai an gudanar da tarutrukan cikin kwararan matakai na tsaro kamar yadda aka saba yi a kowace shekara.