Jami'an Tsaron Iran Sun Dakile Wani Shirin Ta'addanci A Kasar
Ministan tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na kasar Iran Sayyid Mahmoud Alavi ya sanar da cewa jami'an ma'aikatar sun sami nasarar dakile wata makarkashiya ta kai harin ta'addanci a lardin Fars da ke kudancin kasar da wasu 'yan ta'adda 'yan kasashen waje suka shirya kai wa.
Ministan tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na Iran ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da dan jaridar gidan radiyo da talabijin na Iran inda ya ce 'yan ta'addan takfiriyan sun yi shirin kai harin ne a lokacin da ake tarurrukan juyayin Ashura don tunawa da shahadar Imam Husain (a.s), Imamin Shi''a na uku da aka gudanar.
Sayyid Alavi ya kara da cewa bayanan da suka tattaro na nuni da cewa makiya daga waje ne suke jagorantar wadannan 'yan ta'adda da nufin haifar da fitina ta mazhaba da kabilanci a kasar Iran, to sai dai ya ce makiyan sun gaza wajen cimma wannan manufa ta su albarkacin fadakar al'ummar Iran.
A ranar Talatar da ta gabata ma dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran din sun sanar da samun nasarar dakile wani kokari da 'yan ta'adda masu adawa da juyin juya halin Musulunci na kokarin kutsowa cikin Iran ta hanyar lardin Kordestan da ke arewa masu yammacin kasar ta Iran.