Shugaban Kasar Venezuela Nicolás Maduro Moross Ya Iso Kasar Iran
Oct 22, 2016 15:25 UTC
Shugaban Venezuela ya fara ziyarar aiki a Iran
Sa'oi kadan da su ka gabata ne, shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro Moros ya isa Iran domin ziyarar aiki.
A daren yau asabar ne dai ake sa ran shugaban kasar ta Venezuela zai gana da takwaransa na Iran Dr. Hassan Rauhani domin tattauna alakar kasashen biyu.
A jiya juma'a ne dai shugaba Nicolas Maduro ya isa kasar Saudiyya a ziyararsa a kasashe masu arzikin fetur na wannan yankin. Daga cikin kasashen da shugaban kasar zai ziyarta da akwai Qatar da Jamhuriyar Azerbaijan.
Kasar Venezuela tana cikin kasashen da su ke samar da man fetur ga kasuwannin duniya, kuma memba ce a cikin kungiyar Opec.
Tags