Jerin Gwanon Ranar Fada Da Girman Kai Na Duniya A Fadin Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i13348-jerin_gwanon_ranar_fada_da_girman_kai_na_duniya_a_fadin_iran
A yau alhamis ne al'ummar Iran su ka fito kwansu da kwarkwatansu a ranar fada da masu girman kai.
(last modified 2018-08-22T11:29:11+00:00 )
Nov 03, 2016 18:02 UTC
  • Jerin Gwanon Ranar Fada Da Girman Kai Na Duniya A Fadin Iran

A yau alhamis ne al'ummar Iran su ka fito kwansu da kwarkwatansu a ranar fada da masu girman kai.

 Zanga-zangar ta yau tazo ne domin tunawa da ranar 13 ga watan Aban, da daliban jami'oin Iran su ka kwace ofishin jakadancin Amurka da ya ke a matsayin  sansanin leken asiri.

An yi jerin gwano a cikin biranen Ispahan da Tabriz da Kerman da Zahidan  inda aka rika bada taken tir da Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila. Bugu da kari kungiyoyin dalibai da su ka halarci zanga-zangar a cikin garuruwa da birane, sun kona tutocin Amurka.

A nan Tehran, mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya hali, Janar Husain Salamy, da ya gabatar da jawabi a gaban masu zanga-zangar ya ce; Kwace Ofishin jakadancin Amurka da ya ke a matsayin sansanin leken asiri, ya kawo karshen tsoma bakin da Amurkan ta ke yi a cikin siyasar Iran.