An Bude Taron Makon Hadin Kai Karo Na 30 A Tehran
(last modified Thu, 15 Dec 2016 11:12:29 GMT )
Dec 15, 2016 11:12 UTC
  • An Bude Taron Makon Hadin Kai Karo Na 30 A Tehran

A safiyar yau Alhamis ne aka bude taron kasa da kasa kan hadin kan al'ummar musulmi karo na 30 a nan birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, taron da ya sami halartar baki sama da 300 daga ciki da wajen kasar Iran.

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ne ya bude wannan taron mai taken "Hadin Kai Da Wajibcin Fada Da Kungiyoyin Takfiriyya, Masu Kafirta Musulmi".

A jawabin bude taron, shugaba Ruhani ya bayyana cewar Manzon Allah (s) ya umurce mu da mu tsintsiya madaurinki daya kana kuma mu so juna da nuna halaye na kwarai hatta ga sauran mabiya sauran saukakkun addinai na duniya. Har ila yau shugaban na Iran yayi kakkausar suka ga ayyukan ta'addancin da wasu kungiyoyi suke aikatawa da sunan Musulunci yana mai cewa Musulunci ya barranta da irin wadannan ayyuka na su.

Tsawon kwanaki uku da za a yi ana gudanar da taron, malamai da masana da suka fito daga kimanin kasashen 60 na duniya ne za su gabatar da jawabansu kan muhimmancin hadin kai da kuma hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da hadin kai da kuma fada da barazanar da al'ummar musulmi suke fuskanta.

A ranar Asabar ne ake sa ran za a kawo karshen taron inda ake sa ran mahalarta taron za su gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.