Shamkhani: Kudurin Kwamitin Tsaro Zai Kara Ruruta Wutar Rikicin Kasar Syria
(last modified Wed, 21 Dec 2016 18:52:45 GMT )
Dec 21, 2016 18:52 UTC
  • Shamkhani: Kudurin Kwamitin Tsaro Zai Kara Ruruta Wutar Rikicin Kasar Syria

Sakataren Majalisar Koli ta tsaron kasar Iran Ya ce; Kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2328 akan kasar Syria zai kara ruruta wutar rikici.

Sakataren Majalisar Koli ta tsaron kasar Iran Ya ce; Kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2328 akan kasar Syria zai kara ruruta wutar rikici ne a wannan kasa.

Ali Shamkhani ya fada a yau laraba cewa; Kudurin Kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya, mai lamba 2328 an fitar da shi ne ba tare da la'akari da matsalolin da mutanen kasar ta Syria su ke ciki ba ko kuma rawar da gwamnatin kasar ta ke takawa, an yi shi ne domin samarwa 'yan ta'adda mafita.

Ali Shamkhani ya yi ishara da yadda kasashen turai masu amfani da 'yan ta'adda su ka dauki matakai da manufarsu ita ce karfafa 'yan ta'addar, sannan ya kara da cewa: "  Kamata ya yi ace kwamitin tsaron ya maida hankali akan datse hanyoyin aikewa da 'yan ta'adda makamai da kudade, mai makon karfafa su.

Dangane da taron da aka yi a Moscow wanda ya hada ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Turkiya da Rasha, yana sake tabbatar da cewa gwamnatin Syria ce mai cikakken iko da kasarta.